Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 11

Yahaya 11:6-40

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
7Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, “Bari mu je Yahudiya kuma.”
8Sai almajiransa suka ce masa, “Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?”
9Yesu ya amsa, “Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya.
10Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi.
11Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, “Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci”.
12Sai almajirai suka ce masa, “Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka.”
13Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
14Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, “Li'azaru ya mutu.
15Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa.”
16Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, “Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu.”
17Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
18Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su.
19Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu.
20Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida.
21Matta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba”.
22Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka.
23Yesu ya ce mata, “Dan'uwanki za ya rayu kuma.
24Sai Matta ta ce masa, “Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe.”
25Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu;
26Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?”
27Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya.
28Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, “mallam ya iso, kuma yana kiran ki.”
29Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
30Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
31Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
32Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
37Amma wadansun su suka ce, “Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
38Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
39Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
40Yesu ya ce mata, “Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?”

Read Yahaya 11Yahaya 11
Compare Yahaya 11:6-40Yahaya 11:6-40