1To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin.
2Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, “Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba.”
3Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin,
4dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin,
5Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba.
6Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye.
7sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban.
8Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya.
9Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba.
10Sai almajiran suka sake komawa gida kuma.
11Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin.
12Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
13Sukace mata, “Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, “Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba.
14Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane,
15Yesu yace mata, “Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, “Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi.”
16Yesu yace mata, “Maryamu”. Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci “Rabboni!” wato mallam.
17Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku”.
18Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, “Na ga Ubangiji” Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa.
19Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace “Salama Agareku”.
20Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki.
21Yesu ya sake ce masu, “salama agareku. “Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku”.
22Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, “Ku karbi Ruhu Mai Tsarki.
23Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu.”
24Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
25Sauran almajiran sukace masa “Mun ga Ubangiji”. Sai yace masu, “In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba.
26Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, “Salama agareku”.
27Sa'an nan yace wa Toma, “Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya”.
28Toma ya amsa yace “Ya Ubangijina da Allahna!”
29Yesu yace masa, “Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya.
30Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
31Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.