Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya

Yahaya 14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1“Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni.
2A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri.
3In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance.
4Kun san hanya inda zan tafi.”
5Toma ya ce wa Yesu, “Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?”
6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.
7Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi.”
8Filibus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu.”
9Yesu ya ce masa, “Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'?
10Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa.
11Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba.
13Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan.
14Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi.
15“Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina.
16Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada.
17Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku.
18Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku.

19Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu.
20A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku.
21Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi.”
22Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, “Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?”
23Yesu ya amsa ya ce masa, “Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.
24Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take.
25Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku.
26Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku.
27Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata.
28Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma.
29Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata.
30Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na,
31amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.