Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 18

Luka 18:14-42

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi.”
15Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su.
16Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, “Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne.
17Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba.”
18Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce “Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?”
19Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai.
20Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
21Sai shugaban ya ce, “Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta.”
22Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni.”
23Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai.
24Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah!
25Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26Wadanda suka ji wannan magana suka ce, “Idan hakane wa zai sami ceto kenan?”
27Yesu ya amsa, “Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.”
29Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah,
30sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa.”
31Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, “Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata.
32Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau.
33Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi.”
34Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba.
35Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara,
36da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene.
37Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa.
38Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
39Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, “Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
40Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi,
41“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.”
42Yesu ya ce masa, “Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

Read Luka 18Luka 18
Compare Luka 18:14-42Luka 18:14-42