Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 12

Yahaya 12:15-40

Help us?
Click on verse(s) to share them!
15“Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki”.
16Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa.
17Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida.
18Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama.
19Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa “Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa.
20Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin.
21Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, “Mallam, muna so mu ga Yesu.
22Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu.
23Yesu ya amsa masu ya ce, “sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum.
24Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa.
25Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada.
26Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi.
27Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a.
28Uba, ka daukaka sunanka”. Sai wata murya daga sama ta ce, “Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi.
29Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, “Mala'ika ya yi magana da shi”.
30Yesu ya amsa ya ce, “wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku.”
31Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan.
32Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni”.
33Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi.
34Taro suka amsa masa cewa, “Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?”
35Yesu ya ce masu, “Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba.
36Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske”. Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu.
37Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba.
38Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
39Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa,
40ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su.

Read Yahaya 12Yahaya 12
Compare Yahaya 12:15-40Yahaya 12:15-40