Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 20

Luka 20:24-45

Help us?
Click on verse(s) to share them!
24“Nuna mani dinari. Sifar wanene da kuma rubutun wanene akan sa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”
25Sai ya ce masu, “To sai ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma ba Allah, abin da ke na Allah.”
26Marubutan da manyan firistocin ba su sami abin zargi cikin maganarsa, a gaban mutane ba. Suka yi mamakin amsar sa, ba su kuma ce komai ba.
27Sa'adda wadansu Sadukiyawa suka zo wurinsa, wadan da suka ce babu tashin mattatu,
28suka tambaye shi, cewa, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro.
29Akwai 'yan'uwa guda bakwai kuma na farin ya yi aure, sai ya mutu babu da,
30haka ma na biyun.
31Na ukun ya aure ta, haka nan na bakwai ma bai bar yaya ba, har suka mutu.
32Daga baya sai matar ma ta mutu.
33To a ranar tashin mattatu, matar wa za ta zama? Domin duka bakwai din sun aure ta.”
34Yesu ya ce masu, “'Ya'yan duniyan nan suna aure, ana kuma ba da su ga aure.
35Amma wadanda aka ga cancantarsu a waccan tsara, sun isa su sami tashin mattatu, ba za suyi aure ko a aurar da su ba.
36Gama ba za su mutu kuma ba, domin suna daidai da mala'iku kuma su 'ya'yan Allah ne, da shike su 'ya'yan tashin matattu ne.
37Amma batun tashi matattu, ko Musa ma ya nuna wannan, a cikin jeji, inda ya kira Ubangiji, Allah na Ibrahim da kuma Allah na Ishaku da Allah na Yakubu.
38Yanzu shi ba Allahn matattu ba ne, amma na masu rai, saboda duka suna raye a wurinsa.”
39Wadansu marubuta suka amsa, “Malam, ka amsa da kyau.”
40Gama ba su sake yi masa wadansu tambayoyi ba.
41Yesu ya ce masu, “Yaya suke cewa Almasihu dan Dauda ne?
42Gama Dauda da kansa ya ce a cikin littafin Zabura, Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, 'Zauna a hannun dama na,
43sai na maida makiyanka a karkashin tafin sawunka.'
44Dauda ya kira Kristi 'Ubangiji', to ta yaya ya zama dan Dauda?”
45Dukan mutane suna ji ya ce wa almajiransa,

Read Luka 20Luka 20
Compare Luka 20:24-45Luka 20:24-45