Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 13

Luka 13:1-12

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu.
2Sai Yesu ya amsa masu yace “Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka?
3A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu.
4Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka”
6Yesu ya fada wannan misali, “Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba.
7Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, “ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza?
8Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki.
9In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!”'
10Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci.
11Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa.
12Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta.”

Read Luka 13Luka 13
Compare Luka 13:1-12Luka 13:1-12