Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 10

Yahaya 10:5-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
5Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.”
6Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.
7Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki.
8Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
9Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo.
10Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.
11Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa.
12Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su.
13Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.
14Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni.
15Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin.
16Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.
17Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma.
18Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.”
19Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin.
20Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?”
21Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?”
22Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo.
23A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu.
24Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.”
25Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina.
26Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.

Read Yahaya 10Yahaya 10
Compare Yahaya 10:5-26Yahaya 10:5-26