Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 10:5-26 in Hausa

Help us?

Yahaya 10:5-26 in Litafi Mai-tsarki

5 Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba.”
6 Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba.
7 Sai Yesu ya ce masu kuma, “Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki.
8 Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
9 Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo.
10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace.
11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa.
12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su.
13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba.
14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni.
15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin.
16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya.
17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma.
18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana.”
19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin.
20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?”
21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?”
22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo.
23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu.
24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, “Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla.”
25 Yesu ya ce masu, “Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina.
26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
Yahaya 10 in Litafi Mai-tsarki