Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - 2 Tasalonikawa

2 Tasalonikawa 3

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku.
2Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba.
3Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun.
4Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta.
5Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu.
6Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba.
7Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba.
8Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi.
9Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu.
10Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, “Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci.”
11Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu.
12Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su.
13Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai.
14In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya.
15Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa.
16Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.
17Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu.
18Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.