Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 1

Luka 1:67-79

Help us?
Click on verse(s) to share them!
67Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa,
68“Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.”
69Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa,
70kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai.
71Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu.
72Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim.
74Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba,
75a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu.
76I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa,
77domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu.
78Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu,
79domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama.

Read Luka 1Luka 1
Compare Luka 1:67-79Luka 1:67-79