Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 1:67-79 in Hausa

Help us?

Luka 1:67-79 in Litafi Mai-tsarki

67 Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa,
68 “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su.”
69 Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa,
70 kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai.
71 Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu.
72 Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73 rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim.
74 Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba,
75 a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu.
76 I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa,
77 domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu.
78 Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu,
79 domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama.
Luka 1 in Litafi Mai-tsarki