Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 13

Yahaya 13:11-29

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11(Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, “Ba dukanku ne ke da tsarki ba.”)
12Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, “Kun san abin da na yi muku?
13kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake.
14Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu.
15Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku.
16Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba.
17Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su.
18Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'.
19Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne.
20Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni.
21Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni.”
22Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana.
23Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu.
24Siman Bitrus ya ce wa almajirin, “ka fada mana ko akan wa ya ke magana.”
25Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, “Ubangiji, wanene?”
26Sannan Yesu ya amsa, “Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi.” Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
27To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, “Abinda kake yi, ka yi shi da sauri.”
28Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan.
29Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu.

Read Yahaya 13Yahaya 13
Compare Yahaya 13:11-29Yahaya 13:11-29