Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 18

Luka 18:37-43

Help us?
Click on verse(s) to share them!
37Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa.
38Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
39Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, “Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
40Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi,
41“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.”
42Yesu ya ce masa, “Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
43Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.

Read Luka 18Luka 18
Compare Luka 18:37-43Luka 18:37-43