Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 4

Luka 4:9-32

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan.
10Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,'
11kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse.”
12Yesu ya amsa masa cewa, “An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'”
13Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci.
14Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin.
15Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
16Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
17An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
18“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
19in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
20Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
21Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”
22Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, “Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?”
23Yesu ya ce masu, “Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'”
24Ya sake cewa, “Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa.
25Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar.
26Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon.
27Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai.
28Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka.
29Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa.
30Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa.
31Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a.
32Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko.

Read Luka 4Luka 4
Compare Luka 4:9-32Luka 4:9-32