Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 19

Luka 19:32-39

Help us?
Click on verse(s) to share them!
32Wadanda aka aike su suka je sun sami aholakin kamar yadda Yesu ya gaya masu.
33Sa'adda suna kwance aholakin, sai masu shi suka ce masu, “Don me ku ke kwance aholakin?”
34Suka ce, “Ubangiji yana bukatar sa.”
35Suka kawo wa Yesu, suka shimfida tufafinsu akan aholakin sai suka dora Yesu akansa.
36Da yana cikin tafiya, suka shimfida tufafinsu akan hanya.
37Da ya yi kusa da gangaren tudun Zaitun, sai dukan taron almajiransa suka fara yin murna suna kuma yabon Allah da murya mai karfi domin dukan ayukan al'ajibi da suka gani,
38cewa, “Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!”
39Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, “Malam, ka tsauta wa almajiranka.”

Read Luka 19Luka 19
Compare Luka 19:32-39Luka 19:32-39