Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 22

Luka 22:35-64

Help us?
Click on verse(s) to share them!
35Sa'annan Yesu ya ce masu, “Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, “Babu.”
36Ya kuma ce masu, “Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda.
37Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika.”
38Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
39Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi.
40Sa'adda suka iso, ya ce masu, “Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba.”
41Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a,
42yana cewa “Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance.”
43Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi.
44Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini.
45Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu,
46sai ya tambaye su, “Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba.”
47Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba,
48amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?”
49Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?”
50Sai daya daga cikinsu ya kai wa bawan babban firist sara a kunne, sai ya yanke masa kunnensa na dama.
51Yesu ya ce, “Ya isa haka.” Sai ya taba kunnensa, sai ya warkar da shi.
52Yesu yace wa manyan firistoci, da masu tsaron haikali, da dattawa wadanda suke gaba da shi, “Kun fito kamar za ku kama dan fashi, da takuba da sanduna?
53Sa'adda nake tare da ku kowace rana a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan shine lokacinku, da kuma ikon duhu.”
54Suka kama shi, sai suka tafi da shi, suka kawo shi cikin gidan babban firist. Amma Bitrus yana binsa daga nesa.
55Bayan da suka hura wuta a tsakiyar gidan da suka zazzauna tare, Bitrus ya zaune a tsakaninsu.
56Sai wata baranya ta ganshi ya zauna a hasken wuta, sai ta zura masa ido ta ce, “Wannan mutum ma yana tare da shi.”
57Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, “Mace, ban san shi ba.”
58Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, “Kaima kana daya daga cikinsu.” Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ba ni ba ne.”
59Bayan sa'a daya sai wani mutum ya nace da cewa, “Gaskiya wannan mutum yana tare da shi, gama shi dan Galili ne.”
60Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ban san abin da kake fada ba.” Sai nan da nan, da yana cikin magana, sai zakara ta yi cara.
61Yana juyawa, sai Ubangiji ya dubi Bitrus. Sai Bitrus ya tuna kalmar Ubangiji, sa'adda ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau za ka musunce ni sau uku.”
62Da fitowarsa waje, Bitrus ya yi kuka mai zafi.
63Sai mutanen da ke tsare da Yesu suka yi masa ba'a da bulala kuma.
64Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, “Ka yi annabci! Wa ya buge ka?”

Read Luka 22Luka 22
Compare Luka 22:35-64Luka 22:35-64