Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 4

Markus 4:23-33

Help us?
Click on verse(s) to share them!
23Bari mai kunnen ji, ya ji!”
24Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka.
25Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi.”
26Sai ya ce, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa.
27A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba.
28Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko,
29Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan.”
30Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?
31Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya.
32Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta.”
33Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu,

Read Markus 4Markus 4
Compare Markus 4:23-33Markus 4:23-33