Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus

Markus 10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa.
2Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, “dai dai ne mutum ya saki matarsa?” Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi.
3Ya amsa ya ce, menene Musa ya umarce ku?
4Suka ce, “Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita.”
5“Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar,” Yesu ya ce masu.
6Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.'
7Domin wannan dalilin ne mutum zai rabu mahaifinsa da mahaifiyarsa ya mannewa matarsa.
8Su biyu kuwa sun zama jiki daya, ba biyu ba,
9Saboda haka abinda Allah ya hada kada mutum ya raba.”
10Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana.
11Ya ce da su. Dukan wanda ya saki matarsa ya kuma auro wata matar yayi zina da ita kenan.
12Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan.”
13Mutane suka kawo masa 'ya'yansu kanana don ya taba su, sai almajiransa suka kwabe su.
14Da Yesu ya gani, ya ji haushi, ya ce masu. Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su domin mulkin Allah na irinsu ne.
15Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba.
16Sai ya rungume su ya sa masu albarka.
17Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya “Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?”
18Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai.

19Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
20Sai mutumin ya ce masa Malam ai na kiyayye duk wadannan abubuwa tun ina yaro.
21Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni.
22Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai.
23Yesu ya dubi almajiransa ya ce. “Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!”
24Almajiransa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ce masu, ya ku ya'ya'na yana da wuya kamar me a shiga mulkin Allah.
25Zai zama da sauki ga rakumi yabi ta kafar allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah.
26Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, “to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?”
27Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne.
28Bitrus ya ce masa, “to gashi mu mun bar kome, mun bika”.
29Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara,
30sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami.
31Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko.
32Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi.
33“Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai.
34Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi.”
35Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, “Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka”
36Ya ce masu. “Me ku ke so in yi maku?”

37Suka ce, “ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka.”
38Yesu ya ce masu. “Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?”
39Suka fada masa, “Zamu iya.” Yesu ya ce masu, “kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku.”
40Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne.”
41Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.
42Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, “kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko.
43Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.
44Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa.
45Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa.”
46Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya.
47Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, “Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina”
48Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!”
49Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. “Albishrinka, ta so! Yana kiranka.”
50Makahon ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu.
51Yesu ya tambaye shi, ya ce, “me ka ke so in yi maka?” Makahon ya ce, “Malam in sami gani.”
52Yesu ya ce masa. “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare.