Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 26

Ayyukan Manzanni 26:24-32

Help us?
Click on verse(s) to share them!
24Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, “Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka.”
25Amma Bulus ya ce, “Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa.
26Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba.
27Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta.”
28Agaribas ya ce wa Bulus, “A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?”
29Bulus ya ce, “Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin.”
30Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su;
31da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, “Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba.”
32Agaribas ya ce wa Fastos, “Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi.”

Read Ayyukan Manzanni 26Ayyukan Manzanni 26
Compare Ayyukan Manzanni 26:24-32Ayyukan Manzanni 26:24-32