Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 13

Yahaya 13:4-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi.
5Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi.
6Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, za ka wanke mani kafa?”
7Yesu ya amsa ya ce, “Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta.”
8Bitrus ya ce masa, “Ba za ka taba wanke mani kafa ba.” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni”.
9Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina.”
10Yesu ya ce masa, “Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba.”
11(Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, “Ba dukanku ne ke da tsarki ba.”)
12Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, “Kun san abin da na yi muku?
13kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake.
14Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu.

Read Yahaya 13Yahaya 13
Compare Yahaya 13:4-14Yahaya 13:4-14