Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 8

Markus 8:21-38

Help us?
Click on verse(s) to share them!
21Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?”
22Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi.
23Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?”
24Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.”
25Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau.
26Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, “kada ka shiga cikin garin”
27Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, “Shin wanene mutane ke ce da ni?”
28Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, “Iliya”. wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa”.
29Ya tambaye su, “Amma me ku ke ce da ni?” Bitrus ya ce, “Kai ne Almasihu.”
30Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi.
31Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu.
32Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa.
33Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, “Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba.”
34Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, “Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni.
35Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi.
36Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa.
37Me mutum zai bayar amaimakon ransa?
38Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki.”

Read Markus 8Markus 8
Compare Markus 8:21-38Markus 8:21-38