Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 5

Luka 5:29-39

Help us?
Click on verse(s) to share them!
29Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su.
30Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, “Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?”
31Yesu ya amsa masu, “Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita.
32Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba.”
33Sun ce masa, “Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?”
34Yesu ya ce masu, “Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su?
35Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi.”
36Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. “Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba.
37Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace.
38Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna.
39Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, “Tsohon ya fi sabon.”

Read Luka 5Luka 5
Compare Luka 5:29-39Luka 5:29-39