Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 5

Markus 5:9-30

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Ya tambaye shi, “Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa.
10Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar.
11Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni.
12Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun.
13Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa.
14Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru
15Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata.
16Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun.
17Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu.
18Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi.
19Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka.
20Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki.
21Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun.
22Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa.
23Ya yi ta rokonsa, yana cewa, “Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu.”
24Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi.
25Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu.
26Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi.
27Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa.
28Domin ta ce “Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke.”
29Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta.
30Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?”

Read Markus 5Markus 5
Compare Markus 5:9-30Markus 5:9-30