9To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
10Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
11Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
12Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
13Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
14Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
15Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
16Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
17Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
18Babu tsoron Allah a idanunsu.”