Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa

Romawa 16

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya.
2Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma.
3Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu.
4Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai.
5Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya.
6Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru.
7Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni.
8Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji.
9Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena.
10Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus.
11Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji.
12Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji.
13Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni.
14Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su.
15Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su.
16Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku.
17Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su.
18Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi.

19Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta.
20Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku.
21Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana.
22Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji.
23Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu.
24Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin.
25Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa,
26amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka.
27Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin.