Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 1

Yahaya 1:7-17

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa.
8Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken.
9Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya.
10Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba.
11Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba.
12Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah.
13Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah.
14Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya.
15Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, “Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'”
16Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri.
17Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu.

Read Yahaya 1Yahaya 1
Compare Yahaya 1:7-17Yahaya 1:7-17