Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 11

Yahaya 11:41-53

Help us?
Click on verse(s) to share them!
41Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, “Uba, na gode maka domin kana ji na.”
42Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni.”
43Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, “Li'azaru, ka fito!”
44Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, “Ku kwance shi, ya tafi”.
45To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi;
46amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
47Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, “menene za mu yi?” Mutumin nan yana alamu masu yawa.
48Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu.
49Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, “baku san komai ba”.
50Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka.”
51Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar;
52kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya.
53Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu.

Read Yahaya 11Yahaya 11
Compare Yahaya 11:41-53Yahaya 11:41-53