Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 14

Romawa 14:11-17

Help us?
Click on verse(s) to share them!
11Domin a rubuce yake, “Na rantse, “inji Ubangiji”, kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah.”
12Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah.
13Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa.
14Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki.
15Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka.
16Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu.
17Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki.

Read Romawa 14Romawa 14
Compare Romawa 14:11-17Romawa 14:11-17