Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 6

Markus 6:4-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
4Yesu ya ce, “Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa.”
5Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su.
6Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa.
7Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu,
8ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu,
9sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu.
10Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi.
11Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin.
12Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu.
13Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su.
14Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.

Read Markus 6Markus 6
Compare Markus 6:4-14Markus 6:4-14