Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 4

Luka 4:14-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
14Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin.
15Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa.
16Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi.
17An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta,
18“Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci,
19in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji.”
20Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa.
21Sai ya fara masu magana, “Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku.”

Read Luka 4Luka 4
Compare Luka 4:14-21Luka 4:14-21