Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 17

Yahaya 17:15-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
15Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan.
16Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
17Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce.
18Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya.
19Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya.
20Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu,
21Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni

Read Yahaya 17Yahaya 17
Compare Yahaya 17:15-21Yahaya 17:15-21