Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 11

Yahaya 11:32-55

Help us?
Click on verse(s) to share them!
32Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”
37Amma wadansun su suka ce, “Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba?
38Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse.
39Sai Yesu ya ce, “A kawar da dutsen.” Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, “Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa”.
40Yesu ya ce mata, “Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?”
41Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, “Uba, na gode maka domin kana ji na.”
42Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni.”
43Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, “Li'azaru, ka fito!”
44Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, “Ku kwance shi, ya tafi”.
45To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi;
46amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
47Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, “menene za mu yi?” Mutumin nan yana alamu masu yawa.
48Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu.
49Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, “baku san komai ba”.
50Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka.”
51Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar;
52kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya.
53Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu.
54Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa.
55Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su.

Read Yahaya 11Yahaya 11
Compare Yahaya 11:32-55Yahaya 11:32-55