Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 3

Luka 3:3-10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
3Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai.
4Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, “Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa!
5Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada,
6kuma dukan mutane za su ga ceton Allah.”
7Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, “Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu.
9Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta.”
10Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, “To me za mu yi?”

Read Luka 3Luka 3
Compare Luka 3:3-10Luka 3:3-10