Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 6

Markus 6:19-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
19Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba.
20Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi.
21Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili.
22Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”.
23Ya rantse mata da cewa” Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne”
24Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma.
25Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.”
26Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a.
27Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku.
28Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta.
29Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari.
30Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar.
31Sai ya ce da su “ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan,” domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci
32Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai.
33Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo.
34Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa.
35Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, “wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi.
36Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci.
37Amma sai ya ba su amsa ya ce, “Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?”
38Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.”
39Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa.
40Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin.
41Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka.

Read Markus 6Markus 6
Compare Markus 6:19-41Markus 6:19-41