Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Filibiyawa - Filibiyawa 4

Filibiyawa 4:10-14

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba.
11Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi.
12Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata.
13Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.
14Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na.

Read Filibiyawa 4Filibiyawa 4
Compare Filibiyawa 4:10-14Filibiyawa 4:10-14