Text copied!
Bibles in Hausa

Filibiyawa 4:10-14 in Hausa

Help us?

Filibiyawa 4:10-14 in Litafi Mai-tsarki

10 Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba.
11 Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi.
12 Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata.
13 Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.
14 Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na.
Filibiyawa 4 in Litafi Mai-tsarki