Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 11

Ayyukan Manzanni 11:2-13

Help us?
Click on verse(s) to share them!
2Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi;
3suka ce, “Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!”
4Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce,
5Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana.
6Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama.
7Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.”
8Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.”
9Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
10Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
11Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
13Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.

Read Ayyukan Manzanni 11Ayyukan Manzanni 11
Compare Ayyukan Manzanni 11:2-13Ayyukan Manzanni 11:2-13