Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 1

Romawa 1:10-22

Help us?
Click on verse(s) to share them!
10A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah.
11Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku.
12Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku.
13Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai.
14Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima.
15Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma.
16Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa,
17Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, “Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya.”
18Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
19Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
20Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja.
21Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
22Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.

Read Romawa 1Romawa 1
Compare Romawa 1:10-22Romawa 1:10-22