Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Romawa - Romawa 12

Romawa 12:7-17

Help us?
Click on verse(s) to share them!
7In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa.
8Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya.
9Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari.
10Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma.
11Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima.
12Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace.
13Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku.
14Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa.
15Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye.
16Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa.
17Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa.

Read Romawa 12Romawa 12
Compare Romawa 12:7-17Romawa 12:7-17