Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 7

Luka 7:6-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, “Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba.
7Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke.
8Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi.”
9Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, “Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba”
10Daga nan wadanda a ka aika, suka dawo gida suka tarar da bawan cikin koshin lafiya.
11Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa.
12Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita.
13Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, “Kada ki yi kuka.”
14Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi.”
15Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta.
16Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, “An ta da wani annabi mai girma a cikinmu” kuma “Allah ya dubi mutanensa.”
17Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye.
18Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa.
19Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, “Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?”

Read Luka 7Luka 7
Compare Luka 7:6-19Luka 7:6-19