Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 6

Luka 6:6-19

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Ya kasance a wata ranar Asabaci ya shiga cikin majami'a ya kuma koya wa mutane a can. Wani mutum na can wurin wanda hannun damansa ya shanye.
7Marubuta da Farisawa na kallonsa su ga ko zai warkar da wani a ranar Asabaci, domin su samu dalilin zarginsa da yin abin da bai cancanta ba.
8Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, “Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a.” Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan.
9Yesu ya ce masu, “Ina tambayar ku, ya halatta a ranar Asabaci a yi nagarta ko mugunta, a ceci rai ko a hallaka shi?
10Sai ya dube su duka, ya kuma ce wa mutumin, “Mika hannunka.” Ya yi haka, sai hannunsa ya koma lafiyayye.
11Amma suka fusata kwarai, suka yi shawara da junansu game da abin da za su yi da Yesu.
12Ya zama a kwanakin nan, ya hawo bisan dutse domin ya yi addu'a. Ya ci gaba dukan dare yana addua'a ga Allah.
13Da safiya ta yi, ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya kuma zabi goma sha biyu daga cikinsu, wadanda ya kira su “Manzanni.”
14Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus,
15Matta, Toma, Yakubu dan Halfa, Siman, wanda ake kira Zaloti, Yahuda dan Yakubu,
16da Yahuda dan Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.
17Sai Yesu ya gangaro daga dutsen tare da su, suka kuma tsaya a sarari. Almajiransa da yawa na nan a wurin, tare da mutane da yawa daga Yahudiya da Urushalima, da kuma bakin tekun Taya da Sidon.
18Sun zo domin su ji shi, da kuma su sami warkarwa daga dukan cututukansu. Mutane waddan da ke fama da kazaman ruhohi ma sun sami warkarwa.
19Dukan taron jama'ar suna kokarin su taba shi domin ikon warkarwa yana fitowa daga wurinsa, ya kuma warkar da su duka.

Read Luka 6Luka 6
Compare Luka 6:6-19Luka 6:6-19