Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 6

Luka 6:27-44

Help us?
Click on verse(s) to share them!
27Amma ina ce maku ku masu saurare na, ku kaunaci magabtanku, ku kuma aikata nagarta ga wadanda suke kinku.
28Ku albarkaci masu zaginku, ku kuma yi addu'a ga wadanda suke wulakanta ku.
29Wanda ya mare ku a wannan kunci, ku juya masa dayan. Idan wani ya dauki mayafinka, kada ka hana masa taguwarka.
30Ku bayar ga duk wanda ya roke ku. Idan wani ya dauki wani abu da ke naku, kada ku bidi ya mayar da shi.
31Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan.
32Idan ka kaunaci masoyan ka ne kadai, me wannan zai amfane ka? Ko masu zunubi ma na kaunar masoyan su.
33Idan kuna nuna alheri ga wadan da ke maku alheri kadai, menene ladan ku a nan? Ko masu zunubi ma na yin hakan nan.
34Idan kun ba da rancen abubuwa ga mutanen da kuna sa zuciya zasu mayar maku ne kadai, menene ribar ku a nan? Ko masu zunubi suna ba masu zunubi rance, suna kuma sa zuciya a mayar masu dadai gwargwado.
35Amma ku kaunaci magabtan ku, ku kuma nuna masu alheri. Ku basu rance, kada ku sa zuciya a maido maku, kuma sakamakon ku zai zama da girma. Za ku zama yayan Mafifici, domin shi da kansa yana nuna jinkai ga marasa godiya da miyagun mutane.
36Ku zama masu jinkai, domin Ubanku mai jinkai ne.
37Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku.
38Ku bayar ga wasu, ku ma za a ba ku da yawa. Magwaji dankararre, girgizajje har ya cika yana zuba, za su zuba har cinyarku. Domin duk ma'aunin da ku ka yi amfani da shi, da shi za a auna maku.
39Sai ya sake basu wani misali, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Idan ya yi haka, dukansu biyu za su fada cikin rami, ko ba haka ba?
40Almajiri baya fin Malaminsa, amma duk wanda ya samu horo sosai zai zama kamar malaminsa.
41Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba?
42Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka.
43Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya.
44Domin ana iya sanin ko wani itace ta wurin 'ya'yan da yake bayarwa. Domin mutane basu kan tsinki 'ya'yan baure a jikin kaya, ko kuwa su dibi inabi daga jikin sarkakkiya.

Read Luka 6Luka 6
Compare Luka 6:27-44Luka 6:27-44