Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - 1 Korintiyawa

1 Korintiyawa 10

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku.
2Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku,
3kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya.
4Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne.
5Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji.
6Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi.
7Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, “Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa.”
8Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu.
9Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su.
10kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa.
11Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu.
12Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi.
13Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa.
14Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka.
15Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi.
16Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu?
17Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne.
18Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba?

19Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne?
20Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu!
21Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba.
22Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne?
23“Komai dai dai ne,” amma ba komai ke da amfani ba, “Komai dai dai ne,” amma ba komai ke gina mutane ba.
24Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa.
25Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
26Gama “duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne.”
27Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
28Amma idan wani ya ce maka, “Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne” To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri (gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne).
29Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani?
30Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa?
31Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah.
32Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah.
33Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.