Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - 1 Korintiyawa

1 Korintiyawa 11

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu.
2Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku.
3Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne.
4Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa.
5Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski.
6Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta.
7Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce.
8Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take.
9Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji.
10Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku.
11Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
12Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
13Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude?
14Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba?
15Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin.
16To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
17Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce.
18Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar.

19Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku.
20Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
21Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu.
22Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan.
23Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa.
24Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni.”
25Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, “kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni.”
26Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
27Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa.
28Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan.
29In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi.
30Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci.
31Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba.
32In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya.
33Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna.
34Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.