Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - 1 Korintiyawa

1 Korintiyawa 5

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa.
2Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku.
3Gama Kodashike ba ni tare da ku cikin jiki, amma ina tare daku a ruhu, na rigaya na hukunta wanda yayi wannan, tamkar ina wurin.
4Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum.
5Na yi haka ne domin in mika wannan mutum ga Shaidan domin a hallaka jikin, don ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji.
6Fahariyarku bata yi kyau ba. Ko baku sani ba yisti dan kadan ya kan bata dukan dunkule?
7Ku tsarkake kan ku daga tsohon yisti domin ku zama sabon dunkule, wato gurasar da ba ta da yisti. Gama an yi hadayar Almsihu, dan ragonmu na idi.
8Don haka, bari mu yi idinmu ba da tsohon yisti ba, wato yisti irin na rashin tabi'a da mugunta. Maimakon haka, bari muyi bukin idi da gurasa marar yisti ta aminci da gaskiya.
9Na rubuta maku a cikin wasikata cewa kada ku yi hudda da fasikan mutane.
10Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya.
11Amma yanzu ina rubuta maku cewa kada ku yi hudda da duk wanda ake kira dan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko in shi mai ashar ne, ko mashayi, ko dan'damfara. Kada ko abinci ku ci da irin wannan mutum.
12Domin ta yaya zan iya shar'anta wadanda ba 'yan Ikklisiya ba? Maimakon haka, ba ku ne zaku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya ba?
13Amma Allah ke shar'anta wadanda ke waje. “Ku fitar da mugun mutumin daga cikin ku.”