Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 11

Yahaya 11:12-36

Help us?
Click on verse(s) to share them!
12Sai almajirai suka ce masa, “Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka.”
13Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu.
14Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, “Li'azaru ya mutu.
15Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa.”
16Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, “Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu.”
17Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
18Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su.
19Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu.
20Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida.
21Matta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba”.
22Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka.
23Yesu ya ce mata, “Dan'uwanki za ya rayu kuma.
24Sai Matta ta ce masa, “Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe.”
25Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu;
26Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?”
27Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya.
28Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, “mallam ya iso, kuma yana kiran ki.”
29Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa.
30Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi.
31Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
32Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, “Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba”.
33Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma;
34sai ya ce, “A ina kuka kwantar da shi?” Sai suka ce masa, “Ubangiji, zo ka gani.”
35Yesu ya yi kuka.
36Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!”

Read Yahaya 11Yahaya 11
Compare Yahaya 11:12-36Yahaya 11:12-36