13A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima.
14Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru.
15Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su.
16Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba.
17Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki.
18Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?”
19Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane.
20Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi.
21Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru.
22Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe.
23Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai.
24Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.”
25Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
26Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?”