Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Luka - Luka 15

Luka 15:16-23

Help us?
Click on verse(s) to share them!
16Har yayi marmarin ya ci daga cikin barbashin da aladu suke ci, domin babu wanda yake ba shi wani abu ya ci.
17Amma da hankalinsa ya dawo, ya ce, 'Barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe, amma ina nan a nan, ina mutuwa sabili da yunwa!
18Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka.
19Ban cancanci a kara kira na danka ba; ka mai da ni kamar daya daga cikin barorinka.'”
20Sai ya tashi, ya taho wurin mahaifinsa. Amma tun yana daga nesa, sai mahaifinsa ya hango shi tausayi ya kama shi, ya ruga a guje, ya rungume shi, ya yi ta sumbatar sa.
21Dan kuma ya ce masa, 'Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. Ban isa a kara kira na danka ba.'
22Amma mahaifinsa ya ce wa bayinsa, 'Ku yi hamzari ku kawo riga mafi kyau, ku yafa masa. Ku sa masa zobe a hanunsa da takalma a kafafunsa.
23Sa'annan a kawo kiwataccen marakin nan, a yanka. Mu yi buki!

Read Luka 15Luka 15
Compare Luka 15:16-23Luka 15:16-23