Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Markus - Markus 8

Markus 8:6-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
6Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu.
7Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen.
8Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai.
9Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su.
10Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta.
11Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi.
12Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.”
13Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin.
14A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan.
15Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.”
16Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, “Saboda ba mu da gurasa ne.”
17Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?”
18Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba?
19Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.”
20Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, “bakwai.”
21Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?”
22Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi.
23Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?”
24Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.”
25Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau.
26Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, “kada ka shiga cikin garin”

Read Markus 8Markus 8
Compare Markus 8:6-26Markus 8:6-26